1 Nuwamba 2021 - 14:25
​Isra’ila Ta Rusa Gidajen Falasdinawa A Garin Lod Dake Yankunan Falasdinawa Da Ta Mamaye

Rahotanni sun bayyana cewa: “ gwamntin yahudawan sahayuniya ta yi amfani da motocin buldoza tare da rakiyar jami’an tsaro wajen rusa gidajen falasdinawa a yankin al-mahatta dake makwabtaka da birnin Lod da Isra’ila ta mamaye, inda ta rusa gidan wani bafalasdine mai suna Ibrahim Touri, wanda ke da shedar dan kasa a Isra’ila, inda ta yi zargin cewa an gina gidan ne ba tare da Izini ba.

Kamfanin dillancin labarai na Ahlul-Baiti {A.S} - ABNA : A kullum Isra’ila na rusa gidajen fasladinawa a gabar yammacin kogin Jodan babu gaira babau dalili, tana fakewa da cewa an gina su ne ba bisa ka’ida ba ko kuma ba’a nemi izini ba, A wasu lokutan ma takan kubaci falasdinawa su rusa gidajensu ko kuma su biya kudin da za’a rusa,

Kimanin kaso 66 cikin dari na falasdinawa dake rayuwa a manyan biranen tarihi na yankin ne aka tilasta musu barin gidajen su ko aka rusa bayan yakin shekara ta 1948 , Falasdinawa na fuskantar nuna wariya da kyama a Isra’ila kamar yadda kungiyoyin kare hakkin bil adama suka bayyana da suka shaida yadda isra’ila ke rusa gidajensu.

342/